19 Satumba 2014 - 12:57
Majalisar Dinkin Duniya Ta Sanar Da Sabon Shirinta Na Yaki Da Cutar Ebola A Nahiyar Afirka

Majalisar dinkin duniya ta sanar da wani shiri da take das hi na yaki da cutar Ebola a nahiyar Afirka, da nufin dakile kwayoyin cutar baki a nahiyar.

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya sanar da hakan  a jiya a cikin wata wasika da ya aike wa kwamitin tsaron majalisar, inda ya ce bisa la'akari da cewa cutar Ebola ta zama babbar barazana ga rayuwar dan adam, a hakan Majalisar dinkin duniya za ta aike da wata tawaga ta musamman da za ta kunshi kwarrun likitoi da jami'an kiwon lafiya na kasa da kasa zuwa nahiyar Afirka.

 

Ban Ki Moon ya ce tawagar za ta kafa sansaninta a wata kasa da kwayoyin cutar ba su bulla ba, amma kuma za su bude rassu a kasashen da cutar tafi yin yankan kauna, wato Guinea, Liberia da kuma Saliyo, inda za a yi amfani da sabbin dubaru na zamani a bangaren kiwon lafiya shiga yaki da kwayoyin cutar gadan-gadan har sai an ga bayansu. ABNA